Wasanni:- Barcelona ta bada aron Trincao ga Wolves
Kungiyar kwallon kafa ta Wolverhampton ta sanar da sayen fitaccen dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
Trincao ya bugawa Barcelona wasa har sau 43 tun daka sayoshi daga Kungiyar kwallon kafa ta Braga akan farashi €31, in da yaci kwallo biyu kacal ya taimaka wajan cin kwallo sau uku.
Karanta:-Sama da Mutane goma suka rasa rayukansu sanadiyyar hatsari, Kasuwar Bode
Trincao ya bugawa Kasar sa wasanni shida, sai dai babushi cikin Yan wasan da suka buga wasannin gasar cin kofin turai.
A ranar 24 ga watan Juli kungiyar kwallon kafa ta Wolverhampton ta sanar da dauka aron Dan wasan daga Barcelona.
Kungiyar tace tasa ido akan yadda Dan wasan ke taka leda musamman a Yan watanninan da suka gabata.
Yana buga wasa yadda ya kamata tun da kaga Barcelona ta sayoshi daga Braga.
Trincao ya zama Dan wasa na farko da sabon mai horas da Yan kwallon Wolverhampton Bruno Large, bayan ta sallami Nuno Enspirito Santo in da shi Kuma ya koma horas da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a ranar Laraba.