Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta taya Dan wasan gaba na Inter Milan kan dala miliyan 130. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel, na muradin gani Dan wasan ya dawo filin Stamford Bridge don karfafama kungiyar.
Kamar yadda Jaridar Goal, ta wallafa da farko kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan taki amincewa da tayin da Chelsea tayi a kan miliyan dari gami da dan wasan baya Marcos Alonso.
KARANTA:- Kulawa da dokar hanya bata hukumar FRSC kadai bane yana kan kowane mutum
A halin yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na shirye don kawo Dan wasan idan bai wuce dala miliyan dari da talatin ba.
Kamar yadda rahotanni ke zuwa, da yiwuwar kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta sallama masu shi, duba da yanayin rashin kudi da kungiyar ke fuskanta.
Dan wasan Romelu Lukaku ya zauna a Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a tsakanin 2011 zuwa 2013, inda ya buga wasanni sha biyar ba tare da jefa kwallo ko daya ba.
Amma daga baya, bayan ya bar kungiyar ya zamo daya daga cikin manyan Yan wasan gaba wadanda ake tunkaho dasu.
Romelu Lukaku Dan kasar Belgium, wanda ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a shekarar 2017, inda yaci kwallaye 42 cikin wasanni 96.
Sai daga baya Manchester United ta sayar dashi wa Inter Milan akan kudi dala miliyan dari da uku a shekarar 2019, inda tauraruwarsa ta cigaba da haskawa, ya buga wasanni 95 yaci kwallaye 65, inda ya sami nasarar lashe kofin gasar Seria A.