Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Marcus Rashford ba zai samu buga wasanni ba har na tsawon watanni uku biyo bayan matsalar da ya samu a wasannin cin kofin turai daya gabata.
Dan wasan za ayi masa tiyata a kafadar sa hakan zai sanya hanashi buga wasanni na wata uku a kungiyar. Kamar yadda Jaridar Punchnews ta wallafa a shafinta
Dan wasan Marcus Rashford mai kimanin shekaru 23, an aunashi tun baya wanda hakan ya zamar masa matsala a wasannin da yake bugawa.
KARANTA:- Majalisar dokokin Jihar Kano ta gayyaci Muhyi Magaji-Rimingado da ya gurfana a gabanta
Za’a gudanar da yimasa tiyata a karshen watan July saboda ma’aikatan yin tiyatar ba sa nan.
Marcus Rashford ya bugawa Kasar England wasanni biyar a gasar cin kofin turai 2020 inda kuma ya barar da fenariti wanda ya jawoma kasar rashin nasarar cin kofin.
Tun adai ranar ne, kungiyar masu yaki da kabilanci suka fito don kare mutuncin Dan Marcus Rashford kan abinda magoya bayan kwallon kafa ta England keyi akan sa.
Sama da mutane dari ne suka taru suna zana hoton Marcus Rashford tare da sauran abokanan wasanshi su Bukayoko Saka da Jodan Sancho suna nuna kauna da goyon bayan su akan Yan wasan.
Dan wasan Marcus Rashford ya zama zakara tun kamin wasannin, kan irin tallafin da yake na daukar nauyin ciyar da yaran makaranta marasa galihu.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta fara buga wasan sada zumunci ita da kungiyar kwallon kafa ta Derby Country a ranar Lahadi kamin fara kakar wasanni ta Firimiya na wannan shekarar.
Comments 1