Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na son mayarda Dan wasan gefe Eden Hazard zuwa Chelsea kamar yadda ake rade-radin yiwuwar hakan.Pmnews ta wallafa
Dan wasa Hazard duk da yazama gwarzo a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ya koma Real Madrid akan kudi dala $150m. Amma sai dai kwalliya bata biya kudin sabulu ba.
KARANTA:- Dalibai 2 na Bethel Baptist dake Kaduna sun shaki iskar Yanci
Dan wasan ya sha fama da jinya a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wanda hakan bai bashi damar buga wasanni da yawa ba.
Ita dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na fuskantar matsaloli wajan biyan kudin albashin dan wasan, wanda hakan ya hana su dauko wasu sabbin Yan wasan gefe.
Yanzu dai shuwagabannin suna neman yadda za suyi da Dan wasan mai shekaru 30.
KARANTA:- Wata sabuwa: Manyan jiga jigan jam’iyyar PDP guda 4 a Rivers sun koma APC
Sai dai Jaridar Local Report dake Real Madrid ta ruwaito cewar suna tuntubar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea idan za su dawo da Dan wasan duba da Yarjejeniyar da suka kulla na cinikayya da kungiyar.
A halin yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na kokarin sayar da Dan wasan akan 50m. Wanda kungiyar kwallon kafa ta Chelsea take binsu bashi kenan bayan da suka sayi Dan wasan.
Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na haran Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Borusia Dotmund, Earling Halland akan kudin dala 150m.
Comments 1