A yau ranar Talata da gobe Laraba za a fafata wasannin gasar zakarun nahiyar turai wato sabuwar kakar wasa fil tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daban-daban da suke a nahiyar turai kuma da suke buga gasar rukuni-rukuni daban-daban a nahiyar ta turai.
Bayern Munich itace ta lashe kofin a kakar wasa data gabata inda ta lashe gasar sau 6 a tarihi bayan ta sha da kyar a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain daci 1 da nema.
Ga jerin wasannin da za’a fafata a yau Talata:
Lazio da Brussia DorAtalanta.
Barcelona da Ferencavaros.
Chelsea da Sevilla.
Zenit da Club Brugge.
Dynamo Kyiv da Juventus.
Rennes da Krasnodar.
Lazio da Borussia Dortmunt.
RB Leipzig da Istanbul.
PSG da Manchester United.
A gobe Laraba kuwa za a fafata wasanni kamar haka:
Bayern Munich da Athletico Madrid.
Real Madrid da Shaktar.
Salzburg da Lokomotiv Moscow.
Inter Milan da Borussia M’chen Gladbach.
Manchester City da F/c Porto.
Olympiakos da Olympique Lyons.
Midtjylland da Atalanta
Ajax da Liverpool.