Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta sake fitar da wani sabon gargaɗi ga yankunan da ke cikin matuƙar barazanar ambaliyar ruwa a jihar Yobe.
Yankunan da abin ya shafa inji hukumar sun haɗa da ƙananan hukumomin Geidam, Bade, Bursari, Karasuwa, Yusufari da kuma Yunusari.
Babban Daraktan hukumar, Muhammad A. Muhammad shi ne ya fitar da gargaɗin a Damaturu babban birnin jihar yayin wata ziyarar wayar da kai da ya kai jihar.
Shugaban hukumar wanda ya sami wakilcin Dakta Abubakar Suleiman ya ce baya ga lalata gidaje da sauran dukiyoyi, matsalar ambaliyar da ke faruwa kusan a kowacce shekara a bana na barazana ga harkar samar da abinci.
https://dimokuradiyya.com.ng/ambaliyar-ruwa-na-ci-gaba-da-yin-ɓarna-a-jihar-kebbi/
Ya ce ko da yake matsalar sauyin yanayi na taka muhimmiyar rawa wajen kawo ambaliyar, nauyi ne da ya rataya a kan gwamnatin jihar kan ta ɓullo da hanyoyin taƙaita aukuwarta a kowacce shekara.
Hanyoyin a cewarsa sun haɗa da bayar da gargaɗi da kuma ankarar da jama’a a kan lokaci kan barazanar, fitar da shirye-shirye a kan lokaci da kuma ɗaukar matakan kariya.
Shugaban hukumar ta NEMA ya kuma ce hasashen ambaliyar na bana ya nuna cewa aƙalla ƙananan hukumomi 102 daga jihohi 28 su ke cikin barazanar wacce kuma tuni ta fara a sassa da dama na Najeriya.