Wasu Ƴan Daba sun farmaki Tashoshin Motar Akure, sun raunata Ƴan NURTW guda 6
Wasu Ɓata gari da ake zargin Magoya bayan Jacob Adebo da akafi sani da Idajo, sabon shugaban Kwamitin Tashoshin Motoci suka kai farmaki Babbar Tashar Motar Akure, Babban Birnin Jahar Ondo a ranar Litinin, tare da jikkata mutane 6 Ma’aikatan Ƙungiyar Masa Kula da Matuƙa NURTW.
Gwamnan Jahar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya ƙaddamar da Kwamitin Kula da Tashoshin Motoci a ranar Litinin ta hanyar Mataimakin sa Lucky Aiyedatiwa.
Akeredolu ya naɗa Idajo, tsohon Shugaban Ƙungiyar Matuƙa ta NURTW a Jahar, domin jagorantar Kwamitin mai Mutane, wanda ya ƙunshi Fasto na Evengelist Festus Obasoto a matsayin Sakatare.
KARANTA WANNAN LABARIN:;Faransa ta bukaci a bincike gwamnatin sojin Mali kan zargin kashe Fararan hula
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta lura cewa bayan bikin rantsar da Kwamitin, Ɓata gari sun je Tashoshin Motoci da dama tare da farmakar mambobin Ƙungiyar Matuƙa ta NURTW, suke sanyawa Fasinjoji su ruga.
Ɓata garin sun je gidan a saman Motoci da Adduna da Wuƙaƙe da sauran manyan Makamai masu Hatsari, tare da yiwa mutane raunuka da dama da suka farmaka.
Mutane 6 a halin yanzu suna karɓar shan magani a Asibitib Akure.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Funmilayo Odunlami yace har yanzu basu samu rahoton lamarin ba.