Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Juma’a sun kai harin bam a ofishin ‘yan sanda da ke Eika-Ohizenyi a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi.
Yayin harin sun kashe wani dan sanda mai muƙamin wato sufeto Jibril da ke bakin aiki.
Wani mazaunin yankin, Malam Momoh Abubakar, ya bayyana cewa maharan sun mamaye ofishin jami’an ne da misalin karfe 12:15 na safe dauke da bama-bamai da sauran makamai.
Abubakar ya kara da cewa maharan sun samu sarari domin sun shafe sama da awanni biyu suna gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama daga jami’an tsaro ko jama’ar gari ba.
Mazaunin garin ya kara da cewa jami’in dan sanda daya tilo da ke bakin aiki, Jibril wanda aka fi sani da Yellow, ya mutu a harin yayin da motar da ke aiki a ofishin ‘yan sandan ta lalace.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun farfasa gilasan babban masallacin unguwar Eika da cocin Katolika da ke kusa da ofishin ‘yan sanda.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Edward Egbuka, ya ce ya ba da umarnin tura karin jami’an domin aiki, wadanda suka hada da jami’an rundunar ‘yan sandan ko ta kwana, dana sashin yaki da ta’addanci, sashen amsa kiran gaggawa, ofishin leken asiri na jihar tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin dawo da su.