Wasu ɓata gari sun kai hari a Ofishin Ƴan sanda na hedikwata dake ƙaramar Hukumar Onuimo ta Jahar Imo.
Wakilin Majiyar mu ya tattara cewa, sun zo ne da daddare a lokacin da babu wani Jami’in Ɗan Sanda dake aiki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattijai ta tabbatar da naɗin Farfesa Mansur Bindawa a matsayin Kwamishina a Hukumar NCC
Wannan harin da aka kai yazo ne mako guda bayan ƴan ta’adda sun kai hari a ofishin Ƴan sanda na Isu tare da kashe ƴan sanda biyu dake aiki a lokacin.
Wani wanda ya shaida lamarin yayi jawabi akan yadda lamarin ya faru, amma ya buƙaci a sakaye sunan sa, yace ƴan sandan sun kasance suna tafiya gida, sai su buɗe da safe.
Wani ya shaida lamarin yace “mun lura cewa suna tafiya suyi bacci a wani ofishin ƴan sanda. Daren daya gabata, ƴan bindiga sun yi ƙawanya tare da ƙone shi. Shine kaɗai ofishin ƴan sanda dake aiki a yankin, kuma sun ƙone shi. Wannan abun baƙin ciki ne.”
Mai magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar CSP Mike Abattam ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa babu asarar rayuka ko guda ɗaya.