Duba da irin yadda nasara ta ke bibiyar shahararren ɗan wasan nan wato Christiano Ronaldo dangane da wasu ƙwallaye ya jefa a dukkanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da ya bugawa wasanni da suka haɗar da ƙungiyarsa ta farko wato Sporting Lisbon da Manchester United da Real Madrid da kuma ƙungiyar da yake buga wasa a halin yanzu wato Juventus dake ƙasar Italiya.
Haka zalika wasu ƙwallayen ya jefa sune a ƙasar sa ta haihuwa wato Portugal, sai dai a bincikien da jaridar Dimokuraɗiyya ta gudanar dangane da ko wacce ƙwallo da Ronaldo ya jefa, ta gano wasu abubuwa na ban mamaki daga cikinsu. Sai dai kafin mu bayyana abubuwan mamakin zamuyi duba akan adadin ƙwallayen da Ronaldo ya jefa lokacin da yake buga wasa a kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa, zamuyi duba dangane da ƙwallayen da ya jefa a kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafan da ya bugawa wasa.
1. Ronaldo ya buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sporting Lisbon daga shekarar 2002 zuwa 2003 ya buga wasanni 25 inda ya jefa ƙwallaye guda 3.
2. Ronaldo ya buga wasanni 196 a Manchester United ya jefa ƙwallaye 84 daga shekarar 2003 zuwa 2009.
3. Ya buga wasanni 292 a Real Madrid inda ya jefa ƙwallaye 311 daga 2009 zuwa 2018.
4. Ahalin yanzu ya buga wasanni 64 a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus inda ya jefa ƙwallaye 52.
5. Sannan ya buawa ƙasar sa ta Portugal wasanni 165 inda ya jefa ƙwallaye 101.
Ga Abubuwan mamakin game da wasu ƙwallaye da Ronaldo ya jefa kamar haka:
1. Ƙwallon da ya jefa ta ƙarshe a Manchester United lokacin da zaiyi ban kwana domin komawa Real Madrid ya jefa tane ta hanyar bugun tazara wato free kick.
2. Ƙwallon da ya fara jefawa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid itama ya jefa tane ta hanyar bugun tazara.
3. Daga ƙwallaye 311 daya jefa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ƙwallo ta 200 dai dai ya jefa tane ta hanyar bugun tazara wato free kick.
4. Haka idan ba’a manta ba daga cikinsu ƙwallaye 101 da ya jefa a ƙasar da ta haihuwa ta Portugal to cikason ƙwallo ta 100 ya jefa tane ta hanyar bugun tazara da ya jefawa ƙasar Sweden a tsakiyar makonnan a dai dai mintina na 45.