Mazauna Unguwar Masoya Annabi dake cikin Birnin Katsina sun nuna damuwa akan matsalarda suka dade suna fama da ita ta rashin hanyoyin zirga-zirga a unguwar tasu.
Masu magana da yawun al’ummomin ne suka bayyana haka a yayin zantawa da wakilin Jaridar The Fact 24 akan wani aikin gadar itace da suka dauko kuma ya gagare su sabili da rashin karfin tattalin arziki da suke fama da shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu Yanzu: Dalibar Jami’ar Obafemi Awolowo Ta Afka Shalga Ta Mutu
Samar da wannan gada na zuwa ne a sabili da rashin hanya a wannan yanki dake kusa da shataletalen gidan rediyo na companion FM dake Katsina, a sabili da wata korama da ta gitta hanya daya tilo da ake da ita a yankin.
Sai dai abin tausayi a nan shine al’ummar suna amfani ne da gungumen itacen Giginya wurin samar da wata gada domin saukaka masu akan wahalhalunda suke fuskanta sakamakon rashin hanyar.
The Fact 24 ta lura da cewa a halinda ake ciki aikin ya fara gudana amma saboda yanayin tattalin arzikin al’ummar aikin yayi tsaye chik sabili da rashin isassun kudi.
Mazauna Unguwar dai sun maganta akan irin wahalhalunda suke fuskanta a sabili da rashin gadar wanda hakan ya Sanya sukayi tunanin samar da gadar wucin gadi don su samu saukin wahalhalun da suke fuskanta.
A sabili da haka suke roko ga Gwamnatin Aminu Bello Masari da masu hannu da shuni akan su taimaka masu wurin ganin sun ida aikin gadar tare da duba yiyuwar samar da ta din-din-din a yankin.
Al’ummar yankin dai sun taba mika kokon bararsu akan wannan aiki a watanni 6 da suka gabata to sai dai har yanzu hakar su bata cimma ruwa ba.
Don Karin bayani na taimakawa da kayan aiki da abinda Allah SWT ya sauwake sai a nemi wannan lamba:
07033444156
Comments 1