By Ishaq Dabai
Wani faifan bidiyon daya bazu akan shafukan sada zumunta yana nuna yadda wasu baƙi a wurin liyafar aure suke shan gari.
Tun da dadewa, gidajen ma’aurata da yawa na Najeriya suna shan garri,wanda ake samar dashi daga Rogo.
Duk hakan na faruwane Saboda yadda yake da araha, hidimar da ake jiƙa ta cikin ruwa da gyada tare da sukari ana ɗauka cewa a matsayin makoma ta ƙarshe ga iyalai marasa galihu.
A cikin bidiyon da ba a bayyana ba wanda ya bazu a shafin sada zumunta na Tiwita a ranar Juma’a, ana iya ganin yadda baƙi a wajen bikin auren da ba a san su ba suna shagalin shan buɗaɗɗen garri da gyada.
Kazalika a wajen shagalin bikin akwai abubuwan sha masu laushi, ruwan kwalba, da farantin gefe wanda ya zama kamar kifi, ana iya ganin baƙin suna tikar rawa da kiɗan a wajen taron.