…Wasu bankuna sun bi umarnin da babban bankin Kasa CBN ya bayar na su yi aiki a ranekun karshen mako domin.
A ranar Asabar ne aka bude bankunan kasuwanci a birnin tarayya Abuja domin gudanar da kasuwanci kamar yadda babban bankin Najeriya CBN ya umarta.
Majiyar DIMOKURADIYYA ta sa ido a kan wasu bankunan yankin, ya ruwaito cewa an ga dimbin kwastomomi a rumfunan bankunan da ke injin cirar kudi (ATM).
Majiyar DIMOKURADIYYA ta kuma ruwaito cewa an kuma ga kwastomomi a tsaye a kan layi suna shiga dakunan banki daya bayan daya.
KU KARANTA KUMA CBN Ya Umarci Bankuna Da Su Cigaba Da Aiki A Ranekun Karshen Mako
Bankunan da aka bude a kan hanyar Nyanya zuwa Mararaba sun hada da First City Monument Bank (FCMB), United Bank for Africa (UBA), Zenith Bank, First Bank, Fidelity Bank, Ecobank, da Access Bank da dai sauransu.
Misis Ngozi Ugoh, wata kwastoma a bankin Access, ta ce duk da ba ta san wannan umarni na CBN ba, amma ta shiga ne domin samun wasu kudade, sai ta ga dimbin jama’a a bankin ta.
“Ban sani ba game da umarnin buɗewa a karshen mako amma ina wucewa kawai sai na ga mutane don haka na shiga don ganin ko zan iya samun kuɗi,” in ji ta.
Wani abokin ciniki, Mista Andy Jerry da aka gani a bankin Zenith ya bayyana ci gaban a matsayin abin maraba.
Ya yi zargin cewa bankunan na bin umarnin CBN na yin aiki a karshen mako domin dakile shirin gudanar da zanga-zangar da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta shirya gudanarwa babban bankin.
“Ina ganin CBN ta tilastawa bankunan aiki a karshen mako domin kada NLC ta yi zanga-zangar da.ta shirya.
“Ina son wannan saboda zai ba mutane ƙarin lokaci don samun kuɗi,” in ji shi.
Miss Stephanie Ikpe ta yabawa CBN bisa wannan umarnin.
Ta ce wannan ci gaban zai taimaka wajen rage wahalhalun da talakawa ke fuskanta a halin yanzu.
Ikpe ya yi kira ga CBN da ta sanya ido a kan bankunan don ganin an ci gaba da gudanar da ayyukansu a karshen mako.
Babban bankin na CBN a ranar Juma’a ta bakin Daraktan riko na sashen sadarwa, ya bayyana cewa bankunan kasuwanci sun samu makudan kudade a bangarori daban-daban.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Babban bankin ya kuma umarci dukkan bankunan kasuwanci da su bude aiki a ranakun Asabar da Lahadi. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Gwamna Tambuwal Na Sokoto Ya Yi Rashin Kwamishina
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar Sokoto Usman Suleiman Danmadamin Isa ya rasu.
Ya rasu ne a yammacin ranar Juma’a. An ce Isa ya yi rashin lafiya na dan kankanin lokaci.