An tabbatar da mutuwar mutane 6 tare da jikkata wasu da dama bayan wani hari da wasu da ake zargin mayakan al-Shabaab ne suka kai a Mpeketoni da ke gundumar Lamu a kudancin Kenya.
A harin da aka kai da safe a yankin Widhu Majembeni, an kuma kona gidaje da dama da wanda wasu mutane dauke da muggan makamai su ka Kai.
A cewar mazauna yankin da suka zanta da jaridar Nation.Africa, harin na iya kasan cewa na da nasaba da siyasa da ke ci gaba da faruwa a yankin.
“Ta yaya ake zargin ‘yan ta’addar al-Shabaab za su yi amfani da pangas mun san su suna amfani da bindigogi amma wannan harin yana da nasaba da siyasa a kasa. Mun san Mpeketoni na da matukar amfani a siyasar gundumomi idan aka yi la’akari da yawan al’ummarta. Muna son ‘yan sanda su binciki lamarin,” in ji daya daga cikin mazauna yankin.
Kazalika ko da aka tuntubi Kwamandan ‘yan sandan Lamu, Moses Mureithi, ya tabbatar da mutuwar mutanen 6 tare da yin alkawarin yin karin bayani saboda har yanzu wasu nan ba su farfado ba.
“Muna kan wannan batu yayin da muka gano gidaje nawa ne aka kona tare da jikkata mutane. Za mu yi karin bayani nan ba da jimawa ba amma mun killace yankin, yayin da muke kokarin samun wadanda suka aikata laifin,” in ji Mista Mureithi.