Wasu ‘yan baranda da ba a san ko su waye ba sun kai hari a wurin taron jam’iyyar PDP na jihar Zamfara
Majalisar dai za ta baiwa ‘yan jam’iyyar damar zabar zababbun jami’an da za su jagoranci jam’iyyar nan da shekaru uku masu zuwa.
Hakan ya biyo bayan ficewar gwamnan jihar Bello Matawalle daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a kwanakin baya.
‘Yan barandan sun kai hari a wurin taron inda suka fara jifan wasu ‘ya’yan jam’iyyar da ke zaune kafin a fara taron.
Wasu ‘yan bangar siyasa da ba a san ko su waye ba ne suka lalata motoci, kujeru, rumfuna da sauran kayayyaki masu daraja a wurin taron, wanda manufarsu ita ce hana gudanar da taron majalisar.
Mahukuntan jam’iyyar sun ce babu wata tursasawa da za ta hana su gudanar da tarukan jam’iyyar nasu wanda hakkinsu ne a tsarin mulkin kasa.
Jam’iyyar PDP ta Jihar Zamfara ta mayar da taron zuwa wani wurin da ake ganin ya fi tsaro
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Majalisar na ci gaba da gudana a wani wurin da ba a bayyana ba
Kokarin yin magana da ‘yan sanda a jihar ya ci tura domin kakakin rundunar ba ya amsa kiran waya.
Comments 1