Wasu da ba a san ko su wanene ba sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC dake karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu.
Ofishin da ke shedikwatar majalisa a Ogurute ya kone kurmus a daren Lahadi kuma ginin da abin ya shafa ya kone gaba daya.
An tattaro cewa hukumar kashe gobara ta jihar da ke da ofishi a Ogurute ta kasa shiga domin ceto lamarin saboda fargabar sake kai hare-hare har sai an samar da tsaro.
Majiyoyi a yankin sun shaida wa jaridar The Nation cewa a lokacin da aka samar da tsaro, gobarar ta kone ginin gaba daya.
Majiyar ta kara da cewa, abin da motocin kashe gobara biyu daga Nsukka da Ogurute suka iya yi shi ne hana gobarar bazuwa zuwa ofisoshin da ke kusa.
A baya-bayan nan ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai wa Igboeze North da makwabciyarta karamar hukumar Igboeze ta Kudu hari, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe tare da haramtawa masu tuka babura a kananan hukumomin da lamarin ya shafa.