By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 26 da suka hada da yara da mata ne ake fargabar an kashe tare da jikkata wasu da dama a lokacin da wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne dauke da makamai suka kai hari a kauyen Tor-Damisa da ke karamar hukumar Donga a jihar Taraba.
Mazauna yankin sun ce an kona daruruwan gidaje tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira a harin da ya faru da sanyin safiyar ranar Litinin.
Wakilinmu ya tattaro cewa an kai harin ne sakamakon harin da aka kai wa wani Bafulatani a yankin wanda ake zargin wani manomi dan kabilar Tibi ne ya harbe shi a kafarsa.
A halin yanzu dai wanda lamarin ya rutsa dashi yana samun kulawa a hannun ‘yan sanda.
Shugaban al’ummar garin Zaki Umma ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa ana ci gaba da zakulo wasu gawarwaki.
Uma ya bayyana cewa an samu rashin fahimtar juna tsakanin Fulani makiyaya da wasu manoman kabilar Tibi a cikin al’umma kuma ya yi kokarin tara shugabannin Fulani don ganin an dawo da zaman lafiya.
Ya ce, “Wasu manoma sun samu matsala da Fulani makiyaya, amma mun cimma matsaya kuma sun ba mu tabbacin zaman lafiya.
“Na yi mamaki yayin da muka tashi da safiyar yau (Litinin) don ganin an kai hari ga al’ummarmu, wanda ya shafi kauyuka sama da 15.
“Kamar yadda nake magana a yanzu, har yanzu ba mu iya kwato dukkan gawarwakin ba, amma an gano gawarwaki sama da 26.
“Muna cikin wani yanayi na yanke kauna domin ba mu san ko za a ci gaba da kai harin ba. Ina kira ga jihar da ta samar da tsaro tare da shiga tsakani da kayayyakin agaji ga dubban da suka rasa matsuguni.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Usman, mataimakin Sufeton ‘yan sandan, ya ce an kashe mutane shida da suka hada da mace daya, kuma ‘yan sanda sun tura jami’ai zuwa ga al’umma domin wanzar da zaman lafiya.
Ya kara da cewa, “Jami’an sintiri na hadin gwiwa na bataliya ta 93 da ‘yan sanda a yanzu haka suna ta sintiri a dazuzzuka a yankin domin gano maharan.”