By Ishaq Dabai
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin’ yan fashin teku ne a ranar Alhamis sun kai hari tare da yin awon gaba da masunta hudu a Ibaka, karamar hukumar Mbo ta jihar Akwa Ibom.
Wadanda abin ya rutsa dasu ‘yan kasar Ghana uku da dan Najeriya guda daya an ce anyi garkuwa dasu ne a bayan rundunar sojojin ruwa ta Najeriya,a hanyoyin ruwan Ibaka a kan hanyarsu ta zuwa Tekun don balaguron kamun kifi.
Lauyan dake wakiltar wasu masunta, Ogunbiyi Oluwajuwon wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Uyo ranar Juma’a yace ‘yan fashin sun kai hari kan kwale kwale guda hudu sannan suka yi awon gaba da injinansu na waje a cikin wani aiki da suka dauki sa’o’i da dama suna yi.
A cewar Oluwajuwon, masu garkuwar sun nemi a biya su Naira miliyan 2.5 a matsayin kudin fansa kafin a sake su.
Yace “A ranar Talata 28 ga Satumba 2021 da safe masunta daga Ibaka zuwa teku don kamun kifi sun kai hari kan ‘Yan fashin teku dake bayan sansanin sojojin FOB na Najeriya a cikin hanyoyin ruwa na Ibaka kuma sun yi aiki na awanni.
Oluwajuwon wanda ya koka da cewa harin da masu fashin teku ke kaiwa masunta ya zama ruwan dare a yankin, yace wasu masunta sun daina zuwa Tekun saboda tsoron sace su.
“Ayyukan wadannan ‘yan fashin teku sun gurgunta ayyukan kamun kifi a cikin Ibaka da kewayenta kamar yadda Masunta ba zasu iya zuwa kamun kifi ba saboda fargabar farmakin.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Mista .Odiko Macdon lokacin da aka tuntube shi don yin tsokaci ya amsa da cewa, “Ba ni da masaniya har yanzu”