A Amurka wasu daga cikin masu kare tsohon Shugaban Kasar Donald Trump sun sanar da ajiye aikin kare shi daga tuhumar tsige da yan Majlisa suka soma.
Tashar talabijen ta CNN a wani shirin ta ne ta fitar da sunayen wasu lauyoyi biyar daga cikin masu kare tsohon Shugaban kasar Donald Trump da suka sanar da janyewa daga cikin masu kare shi bayan fuskantar rashin fahimta dangane da batun magudi da Trump ke cewa an tafka a lokacin zaben Shugaban kasar da ya baiwa Joe Biden damar lashe zaben shugabancin kasar.