By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara a ranar Asabar din data gabata tace hukumar ta ceci wasu fasinjojin da suka tsalake rijiya da baya yayin da motar bas din su ta kama wuta a daren ranar Juma’a a Ilorin.
Mista Hassa Adekunle,wanda shine jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara da wayar da kan jama’a na jihar ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar, inda yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 19:59, a Kasuwar Challenge Bookshop,dake Unguwar Challenge, Ilorin.
Adekunle yace bas din ta zo Ilorin ne daga Legas a lokacin data kama wuta kuma ta kone sosai.
Ya ce ba’a samu asarar rai ba saboda ‘yan kwana-kwana sun iya dakatar da gobarar a kan lokaci ta yadda suka hana wasu motoci dake yankin konewa.
Adekunle ya bukaci jama’a da kada su yi kasa a gwiwa wajen kiran hukumar kashe gobara domin neman agajin ceto idan wata gobara ta taso a yankunansu.