Fursunoni hudu sun mutu a gidan yarin Najeriya da ke Unguwar Kosere, a Ile-Ife na jihar Osun a lokacin da suka yi yunkurin fasa gidan yarin.
Wani babban jami’in tsaro da bai so a bayyana sunansa ya bayyana haka ga Kamfanin dillancin labaran Najeriya a Ile-Ife ranar Talata.
Jami’in ya ce wasu fursunonin sun shirya tserewa ne a lokacin yin tsafta da safe kuma yayin da suke yunkurin tserewa daga cibiyar, sun jikkata wani jami’in tsaro.
Ya bayyana cewa fursunonin na shirin fita ne yayin da jami’an tsaro suka fatattake su, inda suka kashe hudu daga cikinsu, yayin da wasu da ke son tserewa suka gudu suka buya.
Da aka tuntubi Mista Sola Adeotan, mai magana da yawun Gidajen gyaran hali na jihar Osun, ya ce jita-jita ce, domin babu wani bayani kan lamarin.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Osun, Ms Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta roki karin lokaci domin samun cikakken bayani. (NAN)