Wasu gungun matasa sun yi zanga-zanga a ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma dake jihar Katsina.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a ƙauyukan ɗan Marke da Sanawa da kuma Turare inda matasa suka rufe babbar hanyar Ƙankara zuwa Katsina.
Wani dan kato-da-gora da ke aiki a yankin ya shaida wa majiyar cewa kwanaki biyu da suka wuce ‘yan bidinga sun kai farmaki a kauyukan Kurecinge, Kurecin Malam da Marke da kuma Turare inda suka sace abin hannun mutane sannan suka tafi da wasu.
A cewarsa, hakan ne ya fusata matasa suka fantsama kan tituna domin nuna rashin jin daɗinsu game da yadda gwamnati ta gaza kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar ta Katsina.
https://dimokuradiyya.com.ng/rashin-tsaro-an-sake-yin-wata-sabuwar-zanga-zanga-a-jihar-katsina/
Sai dai daga bisani jami’an hukumar ‘yan sanda sun hallara a wajen da lamarin ya faru domin kauda tarzoma.
Idan ba a manta ba a farkon makon nan ne shugaba Buhari ya bada umarnin sauya fasalin tsarin tsaron ƙasar nan, saboda ganin an daƙile yaɗuwar ayyukan ta’addanci a faɗin Najeriya.
A watannin da suka gabata ma sai da wasu gungun matasa suka yi zanga-zanga a jihar ta Katsina domin nuna rashin jin daɗinsu dangane da yadda gwamnati ta gaza.