Wasu gungun fusatattun matasan IRATE dake babban birnin Akure na jihar Ondo sun kona wata mota bayan salwantar rayukan wasu mutane biyu dake kan babur din Acaba.
Lamarin dai ya shafi wani mai babbar mota, gami da wata karamar mota sai kuma mai babur akan titin Akure-Owo, wanda bashi da nisa da hidikwatar hukumar kiyaye Hadura ta jihar wato Road Safety.
Wani wanda ya ganewa idonsa aukuwar lamari yace wani dan Acaba ne dauke dauke da fasinja ya kaucewa babbar mota,wanda hakan yayi sanadiyyar fadawa hannun da ba nasa, kuma nan take wata mota ta buge su kuma suke ce ga garinku nan.
An dauke gawar wanda suka rasun zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Akure dake jihar ta Ondo.
Da yake tattaunawa da manema labarai, shugaban sashen ayyuka na hukumar kiyaye haduwar na jihar Mista Olusegun Ogungbemide, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ogungbemide ya ce, “al’amarin ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 7 na yamma inda mutum biyu dake kan babur din Acaba suka rasa rayukansu”.
Da yake tattaunawa da manema labarai, kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Tee-Leo Ikoro ya tabbarar da faruwar lamarin sannan yace hukumar tasu ta kama wasu matasa wanda ake zargin suna da sa a hannu a kona motar da aka yi.
Iroko ya ce, “a lokacin da muka isa wajen an kona motar. “
Ya kara da cewa, “muna bincike akan lamari kuma mun yi nasarar cafke wasu da ake zargin suna da hannu a lamarin. “
Daga: Abubakar Muhammad Usman