Kimanin Jiga-jigan Jami’iyyar APC guda 15 suka canja sheka zuwa babbar Jami’iyyar hamayya ta PDP, tare da ɗumbin magoya bayan su a jahar Gombe.
Dayake jawabi ga magoya bayan a sakatariyar jam’iyar PDP, Lazarus Yoriyo tsohon mataimakin Gwamnan jahar, yace baya mamaki da irin abubuwan dake faruwa a jam’iyya mai mulki ta APC, inda ya ƙara dacewa yaga komai dake faruwa.
Yoriyo shine tsohon mataimakin Gwamna Danjuma Goje, wanda yanzu shine Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Matashi ya kashe ɗan uwansa na jini domin yin tsafin kuɗi a Kwara
Kafin zaɓen shekarar 2019, Jami’iyyar PDP itace wadda keda mafi rinjaye a dukkanin jahar, gabanin samun nasarar zaɓen Gwamna Muhammadu Yahaya wanda ya canja yanayin yadda siyasar jahar take ciki.
Acewar Yoriyo, Jami’iyyar PDP zata cigaba da kasancewa Jami’iyyar data fi kowacce nagarta idan akayi la’akari da halin Jami’iyyar APC.
Yace “na shiga Jami’iyyar APC, naga komai yake faruwa a can. Kuma abinda nagani abun bana cigaba bane. Jam’iyyar PDP itace tafi kowacce.”
A lokacin da yake jawabi akan mahimmancin adana katin zabe, tsohon mataimakin Gwamnan ya buƙaci ɗimbin magoya bayan sa dasu kasance cikin shiri, su kuma adana shi.
“Ina son inyi kira ga dubban magoya bayan mu dasu yi ƙoƙari su samu katin zabe gabanin zaɓen shekarar 2023,” inji Yoriyo.
Shima dayake jawabi, Shugaban Jami’iyyar PDP Manjo-Janar Abnor Kwaskebe, ya yaba da ƙudirin masu canja sheƙar zuwa jami’iyyar domin ɗora turbar cigaba.
Kwaskebe yace jahar zata cigaba da kasancewa ta Jami’iyyar PDP, inda yace Jami’iyyar taso tayi amfani da stadium na garin amma hukumomi suka hana.