Wasu jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Sokoto sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Daily Post ta ruwaito cewa, Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar, Hassan Sanyinnawal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a.
Wadanda suka sauya sheka sun kasance jiga-jigan jam’iyyar APC na mazabar Dingyadi-Badawa a karamar hukumar Bodinga.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mun Baiwa Mutane 6,000 Tallafin Naira 20, 000 Kowannensu A Jihar Katsina—Sadiya Umar Farouq
Sun hada da Sakataren Jam’iyar APC a Matsabar, Ummarun Hassan da Jami’in Hulda da Jama’a na Jam’iyar (PRO), a yankin Barno Akamawa.
Sauran sun hada da Mataimakin Ma’aji Manu Abubakar, wakilai hudu – Shehu Abubakar, Sani Modi, Sunusi Imam da Bello Alhaji – da magoya bayansu.
Ana shi bangaren, yayin da yake jawabi wurin tarban su Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bello Goronyo ya yi alkawarin samar da daidaito a tsakanin dukkannin yayan jam’iyyar.
“Dukkanku a yanzu kun zama cikakkun ‘yan Jam’iyar PDP. Ina mai tabbatar muku da cewa za a yi muku daidai wa daida da daukacin mambobinmu a jihar,” kamar yadda NAN ta ruwaito.
A WANI LABARIN KUMA: Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 7 A Jihar Neja
Mutane 7 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Magama da Rafi na jihar Neja. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Babban Daraktan Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Ahmed Ibrahim Inga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya ce an kashe rayuka shida a Magama da 1 a Rafi