Wasu jiga-jigan mutane daga jam’iyyar adawa ta PDP da kuma SDP a Jihar Abia sun saya sheka zuwa APC su da magoya bayan su.
Yan gudun hijiran jam’iyyar sun kuma yi alkawarin cewa za su taimaka wa jam’iyyar izuwa tudun na-tsira a kowane irin hali a shekara ta 2023.
Mutanen sun hada da tsohon mai faɗa a ji Akitet Anagha Mba da Cif Silvanus Nwasu da Barista Chibuike Nwokeukwu gami da Dakta Blessing Nwagba sai kuma tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP.
Da yake karɓar su izuwa jam’iyyar a sakatariyar APC dake birnin Umahiya, Shugaban APC a jihar Abia Honarabul Donatus Nwankpa ya jinjina musu bisa wannan dogon tunani na sauya sheka zuwa APC.
Honarabul Donatus ya alkawarta musu cewa za su samu dul abinda suke bukata ba tare da banbanci ba.