By Abbas Yakubu Yaura
Wasu Jiga-jigan Ƴan siyasa, kuma mashahuran ƴan kasuwa, matasa da samari ƴan Jihar Sakkwato sun ziyarci Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.
Matasan dai masu jini ajika sunyi kiran da babbar murya kan cewa ya kamata gwamnan ya fito ya tsaya takarar Shugabancin ƙasar nan a zaɓen dake tafe na shekarar 2023.
Kazalika matasan sun ce idan akayi la’akari da irin gogewar da gwamnan yake da ita a fagen siyasa da kuma jajircewa wajen ganin cigan al’ummar jihar sa daya ke mulka, suna ganin ya dace ya fito ya tsaya ta kara dan ceto miliyoyin ‘yan Najeriya daga halin kakani kayi.
Matasan sun bayyana hakane alokacin da suka zuyarci gwamnan a fadar sa dake gidan gwamnatin jihar.
Sannan sun kara da cewa irin wannan kiraye kiraye bashine karon farko ba, ko a kwanakin baya ma sai da wasu jiga-jigan siyasar ‘yan jihar Jigawa suka yi masa maka mancin wannan kira don haka suna gani ya dace da wannan matsayin dan fitar da kitse daga wuta.