By Abbas Yakubu Yaura
A yau ne manyan jigajigan siyasar jihar Jigawa karkashin jagorancin Alhaji Abdullahi Rangena Su ka ziyarci Gwamnan Jahar Kogi Dakta Yahaya Bello, tare da yin Kira a gareshi daya fito ya nemi takarar shugabancin Nijeriya.
Mamyan jigajigan siyasar sun bukaci gwamnan ne duba da irin jajircewa da kuma kwarewar da yake da ita afagen siyasa da kuma yadda yake gudanar da mulkinsa wajen tallafawa jama’ar jihar sa ta Kogi.
Abdullahi Rangena yace gwamna Yahaya zai taka muhimmiyar rawa ta siyasa ta fanni daban-daban wajen kawo cigaba a najeriya idan har ya amince da bikatinsu na tsayawa takarar shugaban cin kasar nan.
Tawagar mutanen jigawan dai sun Fito daga kananan hukumomi daban-daban na faɗin jihar inda suka haɗa da shugaban fulanin jihar da kuma shugabar Mata da matasa ta jihar.