Wata gamayyar kungiyoyin farar hula CSO a ranar Talatar nan, sun kada kuri’ar amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan manufar amfani da kudi ba a hannu ba.
Da take yabawa da aiwatar da wa’adin tsohon na Naira da aka sauyawa fasali, kungiyar ta bayyana cewa, manufar wani shiri ne da zai kawar da Najeriya gaba daya daga cin hanci da rashawa, da almundahana da kuma sayen kuri’u. Daily Post ta ruwaito.
KU KARANTA: Abinda Thiago Silva Ba Zai Manta Da Shi A Chelsea Ba
Sai dai kungiyar ta ce ta bankado wani shiri da wasu Gwamnoni 10 ke yi na bujirewa wannan tsari, sakamakon wata gurguwar manufa ta su.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ga manema labarai a ranar Talata, ta ce “wannan manufar na fuskantar suka wadda ta wuce gona da iri daga kungiyar gwamnonin da suka kira kan su da G10, wadanda suka sha alwashin cewa wannan sabuwar manufar baza ta kai su ga ci ba.
Okwukwe wanda ya bayyana goyon bayan kungiyoyin CSO ya kuma bukaci CBN da ta sa ido sosai a kan bankunan da ake raba kudaden.
A wani labarin kuma: Karancin Kudi: Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Hanyar Legas zuwa Abeokuta
Masu zanga-zangar a ranar Talata sun rufe hanyar Legas zuwa Abeokuta da titin Sango-Ota saboda gazawar su na cire kudi daga na’urar cire kudi wato ATM. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Sun yi ta kona tayoyin da ba a amfani da su a bangarorin biyu na babbar hanyar da ta haifar da cunkoson ababen hawa.