Kungiyoyin Fararen Hula guda biyu, a Sanarwar da suka fitar a Jahohin Kano da Anambra a ranar Juma’a sun koka kan yadda aka ware Makudan Kud’ad’e, domin bata sunan Shuwagabancin Kamfanin Matatar Man Fetur ta Kasa wato-NNPC ga Al’umma.
Daya daga cikin Kungiyoyin, sun yi kira ga Shuwagabannin Kamfanin NNPC, da su lura da “masu son bata su da kawo tsaiko a aiyukan su”, inda Kuma suka yi nuni da cewa, suna goyon bayan dokar da Kamfanin NNPC ya kawo, na tabbatar da gaskiya da gaskiya, alhali wasu suna aiki a bayan fage, domin dakatar da hakan.” Inji kungiyar
Kungiyar Kwararru Masu Tabbatar da gaskiya mai suna- Anambra Group Transparency Champions, Karkashin jagorancin Kennedy Micheal, sun bayyana cewa, wasu masu wata manufa “Wanda basa son canje-canjen da akeyi a Kamfanin na NNPC, da jin cewa sun takura a dalilin sake dubi, akan cire tallafin Mai, sai sun yanke shawarar gudanar da gagarumin yaki da Shuwagabancin Shugaban Kamfanin na Kasa Malam Mele Kyari, ta hanyar amfani da Miliyoyin Nairori wurin yin abun da Bai kamata ba.
A na ta bangaren Kungiyar Fararen Hula ta Jihar Kano Mai suna-The Kano Civil Society Organization, Karkashin jagorancin Alhaji Baana Kubwa, sun bayyana cewa, Wanda suka dauki nauyin bata sunan Kamfanin NNPC, basa Farin ciki ne da matsayar kamfanin na yaki da Cin Hanci, da tabbatar da gaskiya da gaskiya, inda suka yi tunanin yakin kawo Karshen haka”. Inji kungiyar.
Sunje suna cewa “Wurin Samar da Man Fetur din, a Karkashin kulawar Shuwagabannin Hukumar na yanzu, wasu Yan Kasuwa ne suka dauki nauyin gudanar da hakan, gami da yin aiki da wasu Ma’aikatan Kamfanin”.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa, cin mutuncin da bata sunan Kamfanin NNPC a yanzu “wasu Ma’aikata ne, na wucin gadi, Wadanda suka fadi Jarabawar ‘Karin girma, shine ya janyo jin haushin, wanda masu yaki da Cire tallafin Man Fetur suka dauki nauyi.”
Kungiyar ta kuma Kara da cewa, wannan gangamin Wanda suka dauki nauyin shafawa Kamfanin bakin fenti, sun fara shine akan matakai “sun fara da Kalubalantar Shuwagabancin Matatar Man Fetur ta Portharcourt, Karkashin jagorancin Manaja-Darakta Ahmed Dikko, inda su kayi imanin yaki da dokar tabbatar da gaskiya da gaskiya a Kamafanin na NNPC.
“Bazu amince da tsofaffin dokoki, da tsare-tsare a ciki da wajen Kamfanin ba, wanda ka’iya kawo tabarbarewar tattalin arzikin mu da hankalin mu”, a cewar Baana.