Kungiyar matasa ta kasa National Youth Council of Nigeria (NYCN), reshen Jihar Kano, da kuma wasu Kungiyoyin Dalibai daban-daban na Jihar Kano, sun kai ziyarar ban girma da nuna goyon baya ga Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero, a fadar sa da ke Bichi, domin nuna goyon bayan su a kan daukaka darajar Masarautun Jihar guda hudu.
Da yake magana da manema labarai a bayan ziyarar na su, shugaban kungiyar a Jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado Lakwaya, ya bayyana cewa, daukaka darajar Masarautun hudu na Jihar Kano, shi ne fatan mafiya yawan mutanan kirki a cikin Jihar ta Kano, ya kuma kara da cewa, ziyarar da matasan suka kai ga Sarkin na Bichi, ta nuna cewa, Matasan na Kano suna goyon bayan daukaka darajar Masarautun da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi.
“Muna da tabbacin cewa, duk abin da gwamnatin Jihar Kano ke yi, tana yin sa ne domin ci gaban rayuwar al’ummar Jihar Kano.
Daukaka darajar Masarautun hudu zuwa Masarautu masu daraja ta daya, yana daya daga cikin abubuwa mafiya kyau da suka faru ga al’ummar Jihar Kano.
Domin nuna goyon bayan mu a kan irin wannan ci gaban ne ya sanya muka yanke shawarar kai irin wannan ziyarar ga dukkanin sabbin Masarautun guda hudu, kamar kuma yanda kuke iya gani, a yanzun mun fara ne da Masarautar Bichi a yau din nan,” in ji Lakwaya.
Hakanan kuma, da yake mayar da jawabi ga matasan, Sarkin na Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nuna dimbin godiyar Masarautar a kan irin goyon bayan da yake samu daga matasan. Sai ya yi kira gare su da su kasance masu son zaman lafiya, su kuma hada kansu a yunkurin da suke yi na daukaka Jihar Kano, kamar yanda suke fata.