Wasu manyan Lauyoyin kasar nan, a Jiya Litinin sun yi fatali da batun bayar da kariya ga Alkalin Alkalan Najeriya da Shugaban Majalisar Wakilai da kuma Shugaban Majalisar Dattawa a daidai lokacin da za a fara kada kuri’a kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar na 1999 a ranar Talata (yau).
Kwamitin wucin gadi na hadin gwiwar Majalisar Dattawa da Wakilai kan sake duba kundin tsarin mulkin kasar na 1999, a ranar Larabar da ta gabata ne suka gabatar da rahotonsa tare da ba da shawarar yin gyare-gyare guda 68, wadanda suka dogara ne kan ‘yan majalisar Tarayya da na zartarwa da kuma bayanan da suka samu daga jama’a a lokacin sauraron jama’a.
A halin yanzu dai shugaban kasa, da mataimakin shugaban kasa, da gwamnoni 36 da mataimakan gwamnoni 36 ne kadai ke da kariya.
Wasu daga cikin Lauyoyin da suka yi hira daban-daban da manema labarai, a ranar Litinin din da ta gabata sun bayyana yunkurin bayar da kariya ga karin jami’an gwamnati da cewa bai kamata ba.
Adegoke Rasheed (SAN), ya ce wannan ba shi ne karon farko da Majalisar Dokoki ta kasa ke yunkurin baiwa shugabannin kariya ba, ya kara da cewa gatan da suke da shi yanzu haka ma ya ishe su.