- Wasu maƙwabta biyu sun yi wani abin da ba a so ba a aurensu ta hanyar musayar matayansu
- Hakan ya fara ne da maƙwabtan sakamakon mazajan na ziyartar matayen a asirce har sai da suka fara jin daɗin juna.
- Daga karshe dai gaskiya ta bayyana kuma mutanen biyu sun zaɓi su sasanta junansu a bisa doka maimakon yin faɗa
Wasu maza biyu da suke makwabtaka da juna sun yi musayar matansu da ‘ya’yansu a wani bikin aure mai ban mamaki.
Afrimax, wanda ta wallafa rahoton faruwar wannan lamarin, ta wallafa wani faifan bidiyo da ya nuna yadda ma’auratan suka sake yin auren bisa doka, inda ta bayyana cewa makwabta ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ta Kashe Sama Da Naira 100,000 A Labulen Ɗakin Da Ta Kama Hanya
Afrimax ta kuma bayyana cewa Lillian ta auri Kelvin sai kuma Immaculate ga Christopher. A matsayin maƙwabta, sun fara ziyartar juna, ba da daɗewa ba suka fara soyayya da ma’aurata.
A asirce suke alakar su, inda mijin waccan yake ziyartar matar maƙocinsa, ashe shima maƙocin yana ziyartar matarsa har sai da aka gano hakan daga baya.
Daga nan sai mutanen suka yanke shawarar sasanta matsalolinsu cikin ruwan sanyi ta hanyar musayar matansu tare da yin hakan a dokance.
Wani bangare na yarjejeniyar shine kowacce mace zata tafi gidan sabon mijin nasu da ‘ya’yanta.
Bidiyon ma’auratan ya jawo martani sosai a shafukan sada zumunta daban-daban.
Kalli bidiyon a NAN https://youtu.be/E_rGLSMRmYY
Ga wasu daga cikin ra’ayoyin da majiyarmu ta tattaro muku:
@LOX.4 ya ce: “Da kun yi haƙuri domin wannan ba komai ba ne.”
@Chansa Jonathan ya ce: “Kana wasa ana wasa da kai. Ba laifi musanya mata.”
@Cher 007 ya ce: “Abin da ubangiji ya hukunta shi ne kawai hukunci.”
@Amundam Marline ya ce: “Na gode da wannan wasan, jan katin.”
@Sassy Selkie72 ya ce: “Muna bukatar mu bi dokokin Allah tun da farko, amma ya yi daidai da ba koyaushe hakan ya dace da al’umma ba.”
@Sophia Cherrington ta ce: “Za a kona su wuta idan sun ci gaba da wauta suna wasa da aure kuma Allah ne ya tsara tsarin aure ba mu ba.”
Nicholas ya ce: “Ni Kirista ne. “Wannan rawar ba al’ummar da Allah ya dora mata ba ne suka sanya ta kada ku rufe matar makwabta.
“A zahiri kamar yadda yake a Exodus sura 20 aya 17.”