• Matar ce ta fara nuna wa matsan uku cewa tana bukatar shiga kungiyar kafin su yi mata ciki.
• Fashikanci da matar na daya daga cikin Ka’idojin da Mabiya Kungiyar ta Hakika suka fada mata kafin ta shiga kungiyar.
• Mijin matar ya ce yayi tafiya zuwa Legas inda ya kwashe sheka Ra daya, da ya dawo sai yaga matarshi da jaririn wata hudu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta cafke wasu matasa uku, mabiya kungiyar Hakika, bisa zargin jan ra’ayin wata matar aure mai suna Zainab Ahmed, inda su kai mata ciki, bisa cewar za su sanya ta cikin tafiyar kungiyar ta harkar.
Wadanda ake zargin su ne, Tukur Dan-Azumi, mai shekara 19, Abubakar Yahuza mai shekara 20, sai Kuma Rufa’i Saosi, mai shekar 27, wadanda dukkanin su, mazauna kauyen Unguwar Dantalle na yankin Tandama dake karamar hukumar Danja.
Rahotanni sun nuna cewa Zainab Ahmed, ta bayyana cewa, “Na sheda masu cewa, ina son in shiga cikin kungiyar ta Hakika, inda suka sheda min cewa, akwai ka’ida daya da zan bin, kafin in shiga harkar, wacce it ace sai sun sadu dani.” inji ta.
A cikin sanarwar da rundunar yan sandan jihar Katsina ta fitar, ta bayyana cewa, “Mijin matar mai suna Isiyaku ne, ya kai wa rundunar rahoton lamarin, inda bayan ya dawo daga jihar Legas, inda ya kwashe shekara daya a can, bayan iso gida kuwa, shine ya iske matarsa da jaririya Mai kimanin wata wata hudu da haihuwa” inji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, bayan da yan sandan jihar suka tuhumi Zainab, ta bayyana musu cewa, “Na nuna sha’awa ta na shiga kungiyar Hakika, inda Matasan suka sheda mun cewa, sai sun yi Fasikanci da ita tukun nan da a matsayin daya daga cikin Ka’idojin shigar ta kungiyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Uba ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyar APC a jihar Anambra
Zainab ta bayyaana cewa, ta amince da ka’ida,r da matasan uku suka gindaya mata, kafin ta shiga harkar.
Sanawar ta kaara da cewa, “Wani mai suna Abdullahi Isiyaku dan shekara 30 da ke a qauyen Wardanga a Karamar hukumar Bakori ya kai kara a caji ofis xin ‘yan sanda na Danja a ranar 17 ga watan Yunin 2021, kan cewa, a wani lokaci a watan Janiarun 2020, ya yi tafiya zuwa jihar Legas, inda ya bar matarsa a gida Mai suna Zainab Ahmed, ‘yar shekara 20, Karkashin kulawar iyayenta da ke a Kauyen Unguwar Dantalle a Tandama cikin Karamar hukumar Danja na cikin jihar Katsina.
Abdullahi Isiyaku ya ce, bayan ya dawo daga Legas a watan Yuni, ya iske matarsa da jaririya Mai kimanin watannin hudu da haihuwa.