Wasan hamayya dai wasa ne da ake bugashi tsakanin wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da suke hamayya da juna inda za a ga wasu a birni ɗaya suke zaune inda wasu kuma biranen da suke zaune daban-daban ne, amma kuma wasu hamayyar tasu takanyi zafi da yawa sosai inda ake rasa rayuka wani lokacin.
Misali wasan hamayya da ake yinsa a kudancin Amurka tsakanin Borca Junior da River Plate wasa ne da har rayuka ake rasawa sosai duba da yadda hamayyar tasu take da zafi sosai kuma wasan yanayin kyawun kallo.
Sai dai muna naganar wasannin hamayya na watan Oktoba dana wata Nuwamba daza a fafata masu zafi kuma wasannin da zasu ɗauki hankalin mutane sosai da sosai kuma ana hasashen wasannin komai zai iya kasancewa musamman yadda kusan kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa tayi gyare-gyare na sayen ‘yan wasa.
Haka zalika a wannan watan na Oktoba za a dawo ci gaba da fafata gasar zakarun nahiyar turai inda a cikin watannin guda biyu za a fafata wasanni masu zafi sosai inda za a fara gasar a ranar Talata 20 ga watan na Oktoba.
Ga jerin wasannin hamayyar daza a fafata a wannan wata na Oktoba da kuma watan Satumba:
1. Za a dawo gasar zakarun nahiyar tirai wato Uefa Champions League.
2. A mako mai kamawa za a dawo gasar abin ƙwararru ta nahiyar turai wato Europa League.
3. A wannan watan na Oktoba za a fafata wasan hamayya mafi zafi a duniya mai taken El Clasico tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da Real Madrid.
4. A wannan rana ta Asabar za a fafata wasan hamayya na cikin gida a gasar ajin Firimiyar Ingila tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton da Liverpool wasan da ake kira da Merseyside derby.
5. Haka zalika a yau Asabar za a buga wasan nan na hamayya a gasar Serra A ta Italiya kuma wasan hamayya na cikin gida tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta A.C Milan da Inter Milan wasan da ake kira da Milan derby.
6. Sannan daga cikin sauran wasannin hamayyar daza a buga a nan gaba akwai wasa tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United da Arsenal.
7. Sannan dai ita kanta Manchester United zata kara da Chelsea a ksana-kwanannan.
8. Sannan dai wasannin basu tsaya nan ba inda a kwanannan za a fafata wasa tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City da Liverpool.
9. Sannan kuma dai a can gasar Bundes Liga ta Janus za a buga wasan nan na hamayya mai taken Der Classica tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brussia Dortmund da Bayern Munich.