Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta samu nasarar bankaɗo maɓuyar wasu maza da suka ƙware wajen yi wa ƙananan yara mata fyaɗe da kuma lalata su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba DSP David Misal ya bayyana yadda aka kama waɗannan mutanen a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.
DSP Misal ya bayyana cewa, “Ahmadu Garba magidanci ɗan kimanin shekaru 65 da haihuwa, na daga cikin waɗanda aka kama bisa zargin lalata da wata ƙaramar yarinyar ‘yar kimanin shekaru 11 da haihuwa. Bayan haka sai Abubakar Bala, ɗan shekara 37 wanda ke sana’ar wankin mota da kuma Suleiman Ahmadu ɗan shekara 28 wanda shima aikin gadi ya ke yi, kuma yarinyar ta yi zama da shi tsawon wata 3 yana lalata da ita a cewarsa.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma ja hankalin iyaye akan su ci gaba da sa ido da kuma maida hankali kan ‘ya’yansu saboda yadda zamani ya lalace.
A baya Mallama Binta Khalid Adam, wata uwa kuma yar fafutukar sauya tarbiyar al’umma ta yi ƙarin haske akan dalilan ƙaruwar ayyukan lalata da kuma fyaɗe ga ƙananan yara da ta kasa su gida uku.
Ta ce kashi na farko sune masu harka da miyagun kwayoyi, na biyu kuma manyan mutane da ke aikata wannan mummunar dabi’a saboda tsubbu. Sai kashi na uku, wanda su kuma hali ne, muddin suka ga wata mace tunaninsu shi ne su keta haddinta.