Wasu fasinjoji mata biyu sun mutu bayan wani hatsarin kwale-kwale a garin Ikorodu na jihar Legas a ranar Larabar nan, kamar yadda hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas (LASWA) ta bayyana.
Babban Manajan Hukumar LASWA, Mista Oluwadamilola Emmanuel, ya bayyana a wata sanarwa cewa kwale-kwalen ya nutse ne nan take bayan ya taso daga tashar jirgin ruwan Ipakodo da ke Ikorodu a Legas.
Emmanuel ya ce jirgin mai daukar fasinjoji 20 mai suna “R & N 2” ya dauki fasinjoji 17, ya kife ne da misalin karfe 7.45 na safe, wanda bai wuce mita 200 daga tashar Ipakodo da ke Ikorodu ba.
Ya ce wasu mata guda biyu da hatsarin ya ritsa da su basu iya ruwa ba, inda aka garzaya da su asibiti mafi kusa domin yi musu magani, amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.
Emmanuel ya ce jami’an tsaron ruwa da kuma tawagar hukumar ta LASWA da aka tattaro zuwa wurin da lamarin ya faru, sun ceto mutane 15 da ransu.
Hukumomin da abin ya shafa dai na binciken matukin jirgin yayin da ake ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan musabbabin afkuwar lamarin har zuwa lokacin da aka bayyana hakan. (NAN)