Rikici ya barke a daren ranar Talata a birnin Kano lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta jihar suka yi artabu da wasu matasa da suka fusata kan yunkurin kwace barasa daga wani wurin sha da siyar da barasa.
Solacebase ta tattaro cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da jami’an Hisbah suka kai farmaki a garin Ballat Hughes ta hanyar Kotu a karamar hukumar Fagge, domin kwace barasa a wanda wata mata ke gudanarwa.
Ba zato ba tsammani, matakin ya harzuka mazauna yankin a Sabon Gari, wadan da galibinsu ba ‘yan asalin yankin ba ne.
Wasu fusatattun ’yan iska sun kai farmaki kan jami’an hukumar Hisbah tare da yin zargin sun kunna wuta da shingaye a fadin yankin.
Shaidu sun ce an samu turmutsutsu a kusa da unguwar Sabon Gari, yayin da bata gari suka yi amfani da damar wajen yin fashi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Gwamnatin jihar Kano ta haramta siyar da kayan maye a cikin jihar yayin da jihar ke aiki da shari’ar muslinci.