By Abbas Yakubu Yaura
Gaba dai gaba dai taurarin gwamnan jihar kogi Yahaya Bello sai kara haskakawa suke a fagen siyasa inda ta ko ina sai samun kiraye-kiraye yake daga sassa daban daban na kasar na neman yafito takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Inda Wasu Jiga-jigan Ƴan siyasa, kuma mashahuran ƴan kasuwa, matasa da samari ƴan Jihar Kebbi da suka ziyarci Gwamna Yahaya Bello na Kogi a ofishin sa dake gidan gwamnatin jihar.
Matasan ‘yan siyasar dai sun bi sahun takwarorin su na jihah Sakkwato wajen neman gwamnan ya fito ya tsaya takarar Shugabancin ƙasar nan a zaɓen dake tafe na 2023.
Kazalika matasan sun ce idan har gwamna Yahaya ya amince da bukatunsu ya tsaya ta kara zasu mara masa baya duba da irin farin jininin daya ke dashi agurin jama’a.
Matasan sunce ba komai ne ya jawo masa wannan farin jinin ba illa kwarewar daya ke da ita wajen iya gudanar da mulki da kuma jajircewa wajen ganin ya kai jama’ar daya ke mulka tudun muntsira.
Sannan matasan ‘yan siyasar sun ce idan akayi la’akari da yadde mutane suke tururuwa tare da yin kiraye-kiraye wajen ganin ya fito ya tsaya ta kara hakan ya nuna yana da tarin magoya baya.