Wani ɗan shekara 56 an bada rahoton yadda ƴaƴen sa guda uku suka kashe shi da duka, sakamakon zargin ɓalla gidan su, tare da satar wayar hannu, da suka saya a tare a Kenya.
Bayan sun kashe mahaifin nasu da duka, sun jefar da gawar sa ,kusa da daji.
Haka zalika, Gawar wasu ƴan mata guda biyu suka ganta akan hanyar su ta zuwa Makaranta.
KARANTA WANNAN LABARIN: AFCON 2021:Karuwai a Ƙasar Cameroon sun fitar da sabon farashi gabanin gasar wasannin cin kofin Nahiyar Afirka
Joyce Nankezho, ƴar uwar marigayin tace ” Marigayin yana da zama a Nairobi, yazo ne binne gawar wani maƙwabcin sa, wanda ya rasu a ƴan kwanakin baya. Yana ɗaya daga cikin wanda suke haƙa kabarin maƙwabcin daya rasu a lokacin da ɗan sa ya kira.”
Kakar yaran Leonida Keya ta bayyana cewa sun zo ne gidan ta domin su ci abinci a ranar da suka aikata lamarin, amma basu faɗa mata abinda suka yiwa mahaifin su ba.
Keya tace “Wannan lamari ya girgiza Ni, na zauna tare da waɗannan yaran, tun lokacin da suka rabu da mahaifin nasu, amma ban taɓa tunanin zasu iya kashe shi ba”.
Kakamega OCPD David Kabeya Wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewar an kama yaran, kuma ana tsare dasu a ofishin ƴan sanda na Kakamega.