By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani mutum mai suna Wasiu Eluyera mai shekaru 35 bisa zargin hada baki da abokinsa Adeniyi Samuel domin kashe tsohuwar matarsa Bola Taiwo mai shekaru 29 da haihuwa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, yace wanda ake zargin yana auren Taiwo, ya rabu da ita ne saboda rashin jituwar da ta samu a tsakanin su.
Ya bayyana cewa Eluyera ya auri wata mata da ke zaune tare da shi yanzu haka.
A cewar Oyeyemi, ya gana da tsohuwar matarsa ne kuma suka sake fita waje, wanda hakan ya sa ta dauki ciki.
Ya ce, “Don gudun kada ya batawa sabuwar matar sa rai, Eluyera ya bukaci Taiwo data zubar da cikin, shawarar da ta ki amincewa da ita.
“Bayan ƙoƙarin da zai iya yi don zubar da ciki bai yi nasara ba, Eluyera ya yanke shawarar kawar da matar da kuma cikin data ke dauke dashi.”
PPRO yace an kama wanda ake zargin tare da wanda ake korafi akansa ne biyo bayan kiran da jami’in ‘yan sanda na sashen, Ogijo, ya samu daga jama’ar da abin ya shafa a ranar 1 ga watan Janairu, 2022.
Oyeyemi yace ‘yan sandan sun tattaro cewa mutanen biyu sun yi mummunan fada ne a yankin Oponuwa da ke Ogijo, kuma idan ba a kama su ba, hakan na iya haifar da zubar da jini.
Ya ci gaba da cewa, “Bayan aikata wannan aika aikar ne, DPO, Ogijo, reshen jihar, CSP Muhammed Baba, ya yi gaggawar tura mutanensa zuwa wurin da lamarin ya faru, inda nan take aka cafke mutanen biyu.
“A lokacin da ake bincike don sanin musabbabin fadan ne Adeniyi Samuel ya bude baki ya sanar da ‘yan sanda cewa Eluyera ya ba shi kwangilar kashe tsohuwar matarsa mai suna Taiwo.
Inda “Ya ci gaba da cewa Eluyera ya yi alkawarin ba shi Naira 10,000 don yin aikin, wanda a ciki ya ba shi Naira 5,000, domin biyan ma’auni inda zai cika masa sauran bayan kammala aikin.
“A cikin sanarwar daya yi ikirari, ya bayyana cewa sau biyu yana siyo mata abinci daga wani gidan cin abinci guda daya kuma sai ya zuba guba a cikin abincin,sannan yake kai mata amma matar ba ta cin abincin.
“Sa’ad da duk ƙoƙarinsa na kashe ta ya ci tura, ya ba Samuel kwangilar taimaka masa ya kawar da ita.
“Ya kara da cewa shi da kansa ya kai Samuel gidan matar, kuma ya ba shi hotonta don ya gane ta cikin sauki.
“Amma da bai aiwatar da aikin ba kamar yadda aka amince da shi, sai ya bukaci a mayar masa da kudin da ya bashi tunda farko, kuma kin amincewarsa ya kai ga fadan wanda a karshe ya kai ga kama su.”
Kazalika PPRO ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin da nufin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.