Wasu mazauna Kubwa da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja, sun koka kan yadda ake zubar da sharar gida ba gaira ba dalili a cikin al’umma, lamarin da ya zama barazana.
Mazauna yankin, wadanda suka zanta da Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, sun bayyana faruwar lamarin a matsayin abin damuwa, inda suka kara da cewa zai yi illa ga lafiyarsu.
Misis Christiana Ezeala, ‘yar kasuwa a Kasuwar zamani ta Kubwa Ultra, ta koka da cewa warin da ke fitowa daga sharar ba shi da kyau kuma yana damun ido.
Ta ce, “mazauna yankin ne suka haifar da lamarin wanda basu nuna damuwa ko kadan ba game da batun rashin kula da barazanar lafiya.”
Karanta kuma: Muna fama da Tsananin rayuwa — Ƴan Shara a Imo sun Koka sakamakon rashin biyan su Albashin wata 5
Ezeala ta kuma yi kira ga gwamnati da sauran hukumomin da abin ya shafa da su nemi hanyoyin magance matsalar da ka iya faruwa.
“Ya kamata gwamnati ta ba da umarni don dakatar da zubar da sharar gida a kasuwa da kewaye, wannan lamarin ya yi muni sosai kuma zai yi illa ga lafiyar mazauna,” in ji Ezeala.
Misis Cordelia Ezeugwu ta ce zubar da shara na sa muhallin ya zama mara dadi da rashin sa lafiya sosai.
Ta ce, “Halin da aka nuna na zubar da sharar ba gaira ba dalili abu ne mai muni kuma mutane za su ji dadin zama a cikin datti, abin da ke da ban tsoro.
“Wannan matakin ya kamata a dauka, mazauna yankin su fahimci cewa mu mutane ne kuma lafiyarmu ita ce ta farko.
“Wannan batu ba gwamnati kadai ba za ta iya kawar da shi ba, duk ya fara ne da mu,” in ji Ezeugwu.
Mista Chibuzor Eloka, Injiniya mai kula da kasuwar zamani ta Kubwa Ultra, ya ce batun sharar wajen kasuwar ya fita daga hannunsa.
Eloka ya ce, “gwamnati ta kuma sha wahala wajen kawar da sharar gida a yau.”
Ya ce manajojin kasuwar suna yin nasu aikin ne ta hanyar daukar manyan motoci a kasuwa tunda ba za su iya biyan kudin tipper ba.
“Mu’amala da mutane ba abu ne mai sauƙi ba. Ko da yake ba mu tilasta zubar da shara ba, babu wanda zai yi biyayya da shi, haka suke.
“Muna iya bakin kokarinmu, matsalar sharar da ake samu a kasuwa daga masu ginin kasuwar ne saboda ba su tsara wurin tara sharar ba.
“Manajoji sun umurci wata babbar mota ta kwashe datti daga muhallin kasuwa zuwa wurin da ba ya damun mutane,” in ji Eloka.
Jennifer Ike, ta ce za a iya kawar da batun ne kawai idan mazauna yankin suka taru suka yanke shawarar “muna son yanayi mai kyau.” (NAN)