Akalla mutane uku ne suka mutu a wani sabon hari da wasu mahara dauke da makamai suka kai a kauyen Tse Ngban da ke unguwar Nyiev Council Ward a karamar hukumar Guma a jihar Benue.
Wasu mazauna garin sun shaida wa Daily Trust ta wayar tarho cewa lamarin da ya faru a daren Lahadin nan ya sa mutanen kauyen barin gidajensu.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wani mazaunin garin da ya bayyana sunansa Abel, ya ce maharan sun yiwa Tseù Ngban kawanya da misalin karfe 7 na dare inda suka yi ta’addanci kan mazauna garin.
Ya ce, “An kashe wata mata a nan take yayin da sauran biyun suka mutu jim kadan bayan harin da aka kai musu sakamakon raunukan da maharan suka yi musu.”
KARANTA KUMA: An Kashe Mutane 5, Yayin Da 10 Suka Bace A Jihar Benue
Abel ya ce a ranar maharan sun tare babbar hanyar Daudu zuwa Lafiya kusa da hukumar NYSC da ke Uda Yagba yayin da suka raunata masu wucewa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benue , SP. Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an kashe mutane uku a harin. Ta kara da cewa an aika gawar marigayan zuwa asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benue.
“An kashe mutane uku a wani hari da aka kai a Guma, an kwashe gawarwaki zuwa BSUTH yayin da ake ci gaba da bincike,” in ji Anene.
A wani labarin kuma: Babbar Kotu Ta Sanya Ranar Hukunci Kan Karar Gwamnatin Tarayya Da ASUU
Babbar Kotun masana’antu ta kasa ta sanya ranar Laraba 21 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan bukatar da gwamnatin tarayya.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Gwamnatin ta shigar da kara a gabanta kan kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) kan dogon lokacin da ta dauka tana yajin aiki.