Wasu Jiga-jigan jam’iyyar PDP biyu a karamar hukumar Kogi, shugaban jam’iyyar mazaba da kuma tsohon mai ba da shawara na musamman, sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a karshen mako.
Shugabannin biyu da suka sauya sheka sune Muhammed Ozahi da Abdulkarim Shaibu Saikayi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Ayarin Motocin Sanata Ifeanyi Ubah
Sannan Sauran biyun su ne tsohon shugaban mazaba na Girinya da KKSE, bi da bi.
Sun sauya sheka tare da dubban mambobinsu.
Kazalika, Hon Ibrahim Usman Egye, wanda kuma tsohon jigo ne a jam’iyyar adawa ya koma APC tare da magoya bayansa daga kabilu daban-daban.
Sauran wadanda su ma suka sauya sheka sun hada da Shugaban kungiyar Vanguard na Next Level, Kwamared Abdullahi Omare Muhammed wanda ya jagoranci wasu ‘ya’yanta zuwa jam’iyyar APC, inda ya bayyana cewa sun yi iya bakin kokarinsu ga jam’iyyar PDP amma ba a basu kyauta ba.
A cewar wadanda suka sauya sheka, sun ga cewa tsarin lada a APC gaskiya ne, ganin cewa ba su amfana sosai ba a lokacin da suke PDP.
“Jam’iyyar APC jam’iyya ce mai cika alkawuran da ta dauka wa jama’a. Ba za mu iya jira ba sai dai mu shiga cikin jirgin kasa mai motsi,” in ji su.
A jawabinsa a wajen bikin, Hon. Bashir Gegu, kwamishinan ma’adanai da albarkatun kasa na jihar Kogi, ya yabawa wadanda suka sauya sheka bisa jajircewar da suka nuna, inda ya dora su kan su kasance masu biyayya ga tsarin, jajircewa da nuna iya aiki ta hanyar yi wa jam’iyyar APC aiki tukuru.
A wani labarin kuma, Ana Fargabar Mutane 13 Sun Mutu A Karin Wani Hatsarin Kwale-kwale A Jigawa
Mutane 13 ne ake fargabar sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.
Rahotanni sun ce lamarin ya afku ne da yammacin ranar Lahadi lokacin da fasinjojin suka shiga cikin wani kwale-kwale daga kauyen Dabi zuwa Sayango domin jajantawa iyalansu kan rasuwar wani dan uwansu.