By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an rufe masana’antar sarrafa shinkafa da yawan noman shinkafa da gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba ya kaddamar na tsawon watanni da dama.
Rahotanni sun ce manoman gida da masu siyar da kaya da masu ba da kaya dake kula da ginin basu da damar shiga wurin
Ziyarar da wakilinmu ya kai masana’antar kwanan nan ya nuna cewa babu wani aiki ko kadan domin an toshe kofar shiga cikin ta. Sannan an gano cewa wasu jami’an tsaro dake bakin kofar Masana’antar wani lokaci suna tursasa duk wanda ke son shiga wurin.
Ita dai Wannan masana’anta na nan ne a wani wuri mai suna Ayade Industrial Estates, inda sauran shirye-shiryen gwamnan suke.sannan yana daya daga cikin ayyukan farko da gwamnan ya kaddamar da shi a wa’adinsa na farko, wanda ya jawo hankalin manyan jami’an gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki na harkar shinkafa da manyan manoma masu zaman kansu.
Wani manomin shinkafa mai suna Ogar Bissong daga Ikom dake tsakiyar jihar yace, “Wata rana na bukaci ganin samfurin irin dana samu domin in saya dan na shuka a gonakina. A bakin kofar aka mayar da ni. Ɗaya daga cikin yaran yace in tafi don kada wani Dr Frank dake kula da wajen kada ya same ni a wurin zan sha mamaki.”
Sakonni da dama da aka yi ta wayar tarho da kwamishinan noma na jihar, Okon Owuna, da kuma shugaban kungiyar manoma shinkafa ta Najeriya (RIFAN), Mista Oliver Ntui, don ya yi tsokaci kan halin da masana’antar ke ciki, har zuwa lokacin kammala wannan rahoton bace komai ba.