By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani babban hakimin Owo, Tunde llori Elerewe kan wani rikicin filaye.
Rahotanni sun bayyana cewa wani babban hakimin wanda aka kai masa hari dai dai amma ya tsallake rijiya da baya, inda ya samu raunuka kuma a halin yanzu an kwantar da shi a cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Owo.
A wani martani daya mayar, gwamna Rotimi Akeredolu ya sha alwashin zakulo wadanda suka kashe wadanda lamarin ya rutsa dashi tare da gurfanar dasu a gaban kotu.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an gayyaci wanda lamarin ya shafa zuwa fadar babban basaraken gargajiya na Owo, Oba Ajibade Ogunoye domin sasanta wani rikicin cikin ruwan sanyi.
Rahotanni sun bayyana cewa babban hakimin ya yi kokarin komawa bayan taron kuma an harbe shi a kusa da wajen.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wata majiya ta nunar da cewa “Wadanda aka farmaka da kuma sauran ’yan bangaren da abin ya shafa suna kokarin komawa garin ne lokacin da wasu mutane suka far musu suka harbe shugaban iyalan har lahira.
Sannan yace babban sarkin ya mutu nan take kuma an tabbatar da mutuwarsa yayin da wani mutum daya da aka harba kuma aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
“Sun ziyarci kadarorin da aka saukar kuma suna komawa garin ne domin mika sakamakon bincikensu ga fadar, sai mutanen suka bayyana gare su suka harbe mutumin da karin wani mutum guda.
“Yan ta’addan sun gudu daga wurin nan take, kuma an kai gawarwakin mutumin da sauran wanda aka harba zuwa asibiti inda daya daga cikinsu ya mutu. Ina tsammanin an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda a garin.
A halin da ake ciki, matasa a tsohon garin sun nuna rashin amincewarsu da kisan gillar da aka yi wa wanda lamarin ya shafa.
Sun tare manyan titunan garin tare da cinna wuta a mahadar First bank, unguwar da mamacin ke da iko kafin a kashe shi.
Matasan sun bayyana kisan nasa a matsayin na dabbanci tare da yin kira da a kamo wadanda suka aikata laifin.