By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga dake sanye da kaki irin na sojoji dauke da makamai da sanyin safiyar Litinin sun far wa ‘yan sanda dake kusa da hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Abia, inda suka kashe wani Insfekta Friday Adama.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, Geoffrey Obonna, ya tabbatar da mutuwar Adama.
Kakakin na ‘yan sandan yace, “Abin takaici ne cewa a ranar 13 ga watan Disamba, 2021 da misalin karfe 01:00 na safe, wasu ‘yan bindiga dake sanye da kaki irin sojoji suka bude wuta kan ‘yan sandan dake bakin aiki a gaban rundunar ‘yan sanda ta 28 dake kusa da hedkwatar rundunar jihar a titin Bende Umuahia.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ’Yan sandan dake cikin shirin ko ta kwana sun mayar da martani ta hanyar harbin ne wanda hakan ya hana ‘yan ta’addan aiwatar da mugun nufi da suka yi kuma suka gudu da sauri da raunukan harbin bindiga.”
Ya kara da cewa Adama ya mutu ne a yayin fafatawar da aka yi da bindiga, ya kuma yi kira ga mazauna jihar da masu kula da cibiyoyin kiwon lafiya dasu “bayar da bayanan kan duk wanda aka samu ko aka gabatar da raunin harsashi ga ‘yan sanda ko wasu Hukumomin tsaro”.
Obonna ya bayyana cewa ba a kai harin ne a hedikwatar ‘yan sanda ba, sai dai ya dakatad da sansanin ‘yan sanda ta wayar tafi-da-gidanka, inda ya bayyana cewa da isar su shingayen binciken na MOPOL da ke wurin, daya daga cikinsu sanye da kakin soji ya sauko ya fara harbi.
Sannan ya bayyana cewa a wani ramuwar gayya, an kuma jikkata daya daga cikin maharan.