By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Imo sun dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wa daya daga cikin ofisoshin su dake Dikenafai a karamar hukumar Ideato ta Kudu a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya ce ‘yan bindigar da suka zo da dama sun kai farmaki ofishin ne da safiyar ranar Alhamis ta hanyar jefa ababen fashewa a cikin ofishin.
Abattam ya ce ba a yi asarar rai ko makamai ba kuma bama-baman da aka tayar sun haifar da barna kadan.
Harin na baya-bayan nan ya zo ne kwanaki kadan bayan na fadar sarkin gargajiya ta Amaifeke da ke karamar hukumar Orlu, Eze E.C Okeke.