By Ishaq Dabai
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani limamin cocin Baptist da kuma wani mutum daya a yammacin Litinin a Lisuru Gida, masarautar Ikulu dake karamar hukumar Zango Kataf ta jihar Kaduna.
Wani mazaunin garin daya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa jaridar PUNCH faruwar lamarin a jiya, inda yace ‘yan bindigar sun bude wuta kan mutanen biyu a kan hanyarsu ta komawa gida daga gonakinsu da misalin karfe 6 na yamma.
Majiyar ta bayyana wadanda ake zargi da cewa Fulani makiyaya ne, inda ta kara da cewa al’ummar na fuskantar barazana.“Fulani sun mayar da gonakin mu wuraren kiwo kuma muna zama cikin barazanar tsaro.
Majiyar tace “al’ummomin dake makwabta koyaushe suna shakkar Fulanin yankin da muke gani a matsayin makwabtanmu ne su.”
Kazalika Ya ce al’ada ta dawo cikin al’umma yayin da yake kira ga gwamnati data ninka kokarinta na ganin an kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin.
A halin da ake ciki, na kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige don yin tsokaci kan lamarin yaci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.