By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar kujerar Sanata dake jihar Jigawa ta Kudu maso Yamma a karkashin jam’iyyar APC, Honorabul Tijjani Ibrahim Gaya, Hajiya Jaja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawal Shisu, wanda ya tabbatar da sace tsohuwar mai kimanin shekaru 70 da haihuwa, kuma an yi garkuwa da ita ne a gidanta da ke garin Kiyawa a karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Sanatoci 3 Sun Kara Ficewa Daga Jam’iyar APC Mai Mulki
Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Litinin din da ta gabata a lokacin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai farmaki gidan dan takarar Sanata a garin Kiyawa da ke karamar hukumar Kiyawa inda suka nunawa wanda abin ya faru da ta karfi kuma suka yi a won gaba da ita.
A cewarsa bayan samun rahoton yin garkuwa da ita, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya hada tawagar ‘yan sanda ta musamman domin ceto wanda lamarin ya rutsa da ita.
DSP Shisu ya bayyana cewa domin tabbatar da kamo wadanda ake zargin da kuma kubutar da wanda abin ya shafa ‘yan sanda suna hada kai da sauran jami’an tsaro domin samun bayanai masu amfani.
Wata majiya daga garin Kiyawa ta shaidawa manema labarai cewa wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane su kimanin 15 zuwa 20 ne suka afka cikin garin dauke da manyan makamai a cikin motoci guda uku da karfin tsiya bayan da suka tsoratar da mutanen da ke kusa da su suka shiga gidan tsohuwar suka dauke ta zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Majiyar ta bayyana cewa har yanzu masu garkuwar ba su tuntubi dangin ba.
Comments 1